Kotu a Malaysia ta wanke Anwar Ibrahim

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Anwar Ibrahim, jagoran 'yan adawa a Malaysia

An wanke jagoran 'yan adawar Kasar Malaysia Anwar Ibrahim daga zargin da ake masa, bayan da aka shafe kusan shekaru biyu ana masa shari'a.

An dai zargi Mr. Anwar da yin lalata da wata tsohuwar ma'aikaciyarsa, amma wani Alkali ya yanke hukuncin cewar gwajin da aka yi na DNA bai tabbatar da wannan zargi ba.

Dubun dubatar Magoya bayan Mr Anwar dai sunyi farinciki da wannan hukunci a wajen kotun dake birnin Kuala Lampur.

Mr. Anwar dai ya bayyana cewar gaskiya ce tayi halinta.

Wakiliyar BBC tace gwamnatin Kasar ta shafe fiye da shekaru hamsin akan mulki, kuma Mr Anwar shine kadai mutumin da yake iya kalubalantar gwamnati.