Shugaban ma'aikata a fadar white ya ajiye aiki

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Barack Obama da Mr Bill Daley

Yayinda ya ragewa Shugaba Obama na Amurka watanni goma kafin ya sake tsayawa takarar zaben shugaban Kasa, Shugaban ma'aikata na fadar white house Bill Daley ya sauka daga kan mukaminsa.

Shugaba Barak Obama ya ce Mr Bill dai ya yanke shawarar barin aikinnasa, bayan daya shafe shekara guda cif akan aikin.

Ya kuma bayyana shi a matsayin mutum mai kwazon aiki. Masu aiko da rahotanni sun bayyana saukar tasa a matsayin wani abun daya zo da mamaki.

Jack Lew dai, shine zai kasance sabon Shugaban ma'aikatan fadar ta white house, kuma yanzu shike ke lura da sha'anin kasafin kudi.

Shugaba Obama ke nan yake cewar ina farin cikin sanar daku cewar Jack Lew ya amince ya karbi mukamin sabon shugaban ma'aikata

Ana daukar wannan kujera ta Shugaban ma'aikata dai da mahimmanci sosai a siyasar Amurka.