Amurka ta zargi Iran game da inganta Uranium

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Cibiyar nukiliya da ke Qom

Amurka tace shirin da Iran take yi na inganta makamashin Uranium zuwa kusa da matakin samar da wani makami ya saba kudurin majalisar dinkin duniya.

A ranar Litinin Hukumar makamashi ta duniya ta tabbatar da cewar Iran ta soma inganta Uranium din zuwa kashi ashirin da biyyar cikin dari, a wata tashar ta, dake karkashin kasa a tsaunukan dake kusa da Qom

Iran dai tace tana bukatar tayi hakan domin samar da maganin cutar cancer ko kuma daji

Ofishin kula da harkokin wajen Amurka ya yi kira da Iran da ta tsaida inganta makamashin na Uranium, kuma ta bada hadin kai ga Humar Sa'ido ga Makamashin Nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA.

Iran ta dakata

Mai magana da yawun Ofishin kula da harkokin wajen Amurka, Victoria Nuland ta ce yawan makamashin na Uranium da Iran ke sarrafa ya kara sa shakku a zakutan jama'a cewa ba wai za ta yi amfani da shi bana na ayyukan ci gaba.

Ta ce za'a iya amfani da ingancin Uranium din da ya kai kashi ashirin zuwa makaman nukiliya.

Sakatare kasashen wajen Burtaniya, William Hague ya ce matakin da Iran ta dauka ya harzuka mutane da dama a dai dai lokacin da kasashen duniya ke bukatar Iran ta basu tabbacin cewa zata amfani ne da makamashin nukiliya domin ci gaba.

A 'yan kwanakin nan dai ana takun saka tsakanin gwamnatin Iran ne da kuma kasashen yamma.

A makon daya gabata, sai da gwamnatin Amurka ta kakabawa babban bankin Iran takunkumi, a yayinda itama kungiyar tarrayar Turai ta yi barazanar sanya takunkumi kan man da kasar ke fitarwa.