Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun lashi takobi

Nigeria Protest
Bayanan hoto,

Nigeria Protest

Dubban jama'a a Najeriya sun shiga zanga zanga don nuna adawa da tsadar man fetur, bayanda gwamnatin kasar ta janye tallafinda ta ke baiwa bangaren man.

Ana kuma gudanar da yajin aikin gamari a kasar.

Zirga zirgar ababen hawa ta tsaya cik, kuma an rufe shaguna da ofisoshi.

Kungiyoyin kwadago sun ce yajin aikin ya zama dole kuma ba zasu tattauna da gwamnati ba saboda basu yadda da ita ba.

'Yan sanda sun yin amfani da barkonon tshohuwa don tarwatsa masu zanga zanga a birnin Kano, kuma an rawaito cewa an harbe daya daga cikin masu zanga zangar har lahira a Legas.

'Yan Najeriya dadama dai na ganin tallafin a matsayin shine kadai, amfanin da suke samu daga gwamnati, yayinda kuma ita gwamnati ta ce babu yadda za'a yi tallafin ya dore.