An kai hari kan wani masallaci a Benin

Najeriya
Image caption Najeriya na fuskantar tashe-tashen hankula daban-daban a yanzu

An kona wani masallaci da makarantar Islamiyya a wani hari da wasu mutane suka kai a birnin Benin na jihar Edo a Kudu maso Kudancin Najeriya.

'Yan sanda sun shaida wa BBC cewa an kashe mutum guda a harin, inda aka kama mutane 10.

Wannan dai ya biyo bayan wani hari ne da aka kai kan wani masallaci a birnin ranar Litinin.

A 'yan kwanakin nan an kai hari kan al'ummar Kirista a Arewacin kasar - wanda ake dora alhakinsu kan kungiyar nan ta Boko Haram.

Wani jagoran Hausa a birnin Benin ya shaida wa BBC cewa 'yan asalin Arewacin kasar kimanin 7,000 ne ke neman mafaka a barikokin 'yan sanda da na soji a birnin.

Jama'a na yin kaura

Kungiyar agaji ta Red Cross ta tabbatarwa da BBC cewa suna samun Hausawa da ke neman mafaka a wuraren 'yan sanda da sojoji.

'Yan sanda sun ce an kuma kona motoci biyu da ke ajiye a Cibiyar wacce ke dauke da masallaci da makarantar Islamiyya.

Wannan ne hare-hare na baya-bayan nan masu alaka da addini da kabilanci da ake kaiwa a kasar wadanda suka yi sanadiyyar 'yan kudanci da dama barin arewacin kasar.

Suma 'yan arewacin kasar da dama sun bar kudancin domin tserewa da rayukansu.

Image caption Farfesa Wole Soyinka ya ce lamarin ya wuce yadda ake zato

Shahararren marubucin nan dan Najeriyar Farfesa Wole Soyinka, ya dora alhakin rikicin kan shugabannin da ke fifita addininsu kan hadin kan kasa.

"Idan a kasa har an kai matsayin wasu mutane za su je wuraren ibada su bude wuta ta taga, to lalle abun ya kai matuka", kamar yadda ya shaida wa BBC.

Mista Soyinka ya ce wasu shugabannin siyasar kasar ba za su yadda su zauna a karkashin wani addini daba na su ba.

"Wasu 'yan siyasa na yin amfani da kungiyoyin addini ne kawai don kawarda tunanin jama'a daga muggan abubuwan da suka aikata, kamar yin sama da fadi da dukiyar jama'a", a cewar Soyinka.

Karin bayani