Shugaba Assad ya soki kasashen waje

Shugaba Assad na Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Har yanzu ana ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnatin Syria

Shugaban Syria Bashar al-Assad ya zargi kasashen waje da kokarin dagula al'amura a kasar, a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da mulkinsa.

"A zahiri ta ke cewa akwai hadin bakin kasashen waje," a cewar Assad, a jawabinsa na farko a bainar jama'a cikin watanni da dama.

Ya ce za a gudanar zabe nan gaba a bana sai dai ya kara da cewa "'yan ta'adda" za su gamu da "fushin hukuma".

Kungiyar kasashen Larabawa ta ce tana dora alhakin harin da aka kaiwa jami'anta da ke sa ido kan gwamnatin Syria.

A wata sanarwa da suka fitar a ranar Talata, Sakatare Janar na kungiyar Larabawa Nabil al-Arabi ya yi Allah wadai da "rashin sanin ya kamata da hare-haren da ake kaiwa masu sa ido na kungiyar" a Syria.

Mr Arabi ya ce an jikkata wasu daga cikin masu sa ido na kungiyar a hare-haren da masu goyon baya da kuma adawa da gwamnati suka kai musu.

Karin bayani