An kama makamai da za'a kai Najeriya

Harsasai masu rai
Image caption Harsasai masu rai

Rahotannin da ke fitowa daga Ghana na cewar, 'yan sanda a birnin Accra sun kama wata babbar mota makare da bindigogi da kuma harsasai, wadda ke kan hanyarta zuwa Najeriya.

Babbar kwamandar 'yan sanda da ke kula da jihar Accrar, DCOP Rose Atingah Bio ce ta bayyana hakan.

Ta ce, sun kama motar ce jiya da yamma, tare da wasu 'yan Najeriya biyu da 'yan Ghana uku da ke cikinta.

Karin bayani