Japan za ta rage shigo da mai daga Iran

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jun Azumi, Ministan kudin Japan da kuma Sakatere bailtul malin Amurka, Timothy Giethner

Ministan kudin Japan Jun Azumi yace kasarsa zata dauki kwararan matakai domin rage yawan man da take shigowa dashi cikin Kasar daga Iran.

Kasar Japan dai ta dogara ne a kan Iran da kusan kashi goma cikin dari na man da take amfani da shi.

Kasar sai na bukatar man soasi domin samar da wutan lantarki a kasar saboa matsalar da aka samu a cibiyar nukiliya ta Fukushima.

Amma bayan ya gana da Sakataren baitul malin Amurka, Tomothy Geithner Ministan kudin Japan Jun Azumi ya ce kasarsa za ta rage yawan man da take shigowa da shi daga Iran.

Japan ita ce kasa ta biyu mafi girma dake sayan mai daga Iran, kuma tuni ta bukaci kasashen yankin Gulf da su kara yawan man da suke fitarwa.

Amurka dai na bukatar Japan ta bada hadin kai dangane da takunkumin da za a sanyawa Iran a bangaren man ta.

Amurkawa sunce Iran taki daukar mataki game da damuwar da ake nunawa kan shirinta na nukiliya wanda ake ta takaddama da akai.

Kuma tuni dama Mr. Geithner ya kai irin wannan ziyara zuwa China, kasar da tafi kowace Kasa a duniya sayan man Iran, amma jami'ai a can sunce ba a tsammanin Chinan za ta amince da bukatar Amurkan.