Boko Haram ta ce babu abunda jami'an tsaron za su iya yi mata

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto youtube
Image caption Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau

A Najeriya, Kungiyar nan ta Boko Haram ta saki wani hoton bidiyo wanda a cikin sa ta kare hare-haren da ta kai kwanan nan a wasu sassan arewacin kasar.

A hoton bidiyon wanda aka wallafa a shafin youtube, an nuno shugaban kungiyar Malam Abubakar Shekau shanye da rawani da kuma rigar sulke yana zaune tsakanin bindigogi biyu.

A jawabin, mai tsawon minti 14, Shekau ya ce an kai hare-haren ne don ramuwar gayya saboda kashe Musulmin da aka yi a sassan arewacin Najeriya.

A jawabin nasa mai taken ''Sako zuwa ga Shugaba Jonathan'', Shekau ya ce jami'an tsaron kasar ba za su iya hana 'yan kungiyar kai hare-hare ba.

Kungiyar dai ta kai jerin hare-hare a kasar, ciki har da wanda aka kai ranar kirsimati a wajen wata majami'a a kusa da Abuja wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane talatin da bakwai.

Sasantawa

A sakon nasa Malam Abubakar Shekau ya ce koda zasu sasanta, to sansantawar zata kasasn ce ne a bisa koyarwar Al-Qur'ani da hadisi.

Wannan hoton bidiyon dai zai tada wa hukumomin kasar hankali, ganin yadda can dama kasar ke fama da matsalar tsaro.

Kungiyar boko haram din dai ta tsananta kai hare hare akan mabiya addinin kirista a arewacin kasar, da a kwanakin baya ta ce su fice daga yankin.

Karin bayani