Wasu 'yan bindiga sun kashe mutane takwas a Potiskum

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Taswirar Najeriya

Wasu 'yan bindiga a Najeriya sun kashe mutane takwas da suka hada da jami'an 'yan Sanda, a lokacin da suka bude wuta kan wata mashaya a garin Potiskum dake arewacin Kasar.

Wannan shine jerin hare- hare na baya bayannan da jami'ai suka dorawa kungiyar nan ta Boko Haram alhakin kaiwa.

Tunda a jiya ma dai an kashe akalla mutane biyar a lokacin da aka cinna wuta kan wani masallaci da wata makarantar Islamiyya a birnin Benin dake kudancin Najeriyar

Ya ce ina tunanin wasu ne ke cike da bakin cikin kashe- kashen da 'yan Boko Haram ke yi a Arewacin Kasar. Ina tunain abinda ya harzuka mutane kenan a nan

Musulmi dai a yanzu na ta kauracewa birnin zuwa arewacin Kasar.

Zaman dar- dar na addini dai na karuwa, yayinda kungiyar Kwadagon kasar ke cigaba da yajin aiki sakamakon tashin farashin mai.

Karin bayani