Mitt Romney ya yi nasara a New Hampshire

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon gwamnan, Masachusets Mitt Romney

Mitt Romney ya kara karfafa matsayinsa a matsayin dan takarar dake kan gaba na neman kujeran shugaban kasa a jam'iyyar Republican.

Idan ya yi nasara dai zai fafata ne da Shugaba Barack Obama a zaben shugaban Kasar Amurka da za a yi a watan Nuwamba.

Dan takarar dai ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar Republican a New Hampshire.

Tsohon gwamnan na Masachusets Mr Roomney, yasha gaban abokin hamayyarsa Ron Paul da akalla maki goma.

A wani jawabi da yayi wa magoya bayansa, Mr Roomney ya soki tsarin tattalin arzikin Shugaba Obama.

Bayan nasarar da ya samu a makon daya gabata, yanzu za a fafata da Mr. Roomney a South Carolina daga bisani a cikin wannan watan.