Rana ta uku ta yajin aiki a Najeriya

Rana ta uku ta yajin aiki a Najeriya Hakkin mallakar hoto 1

A Najeriya adadin jama'ar da suka fito kan tituna domin zanga-zangar adawa da janye tallafin mai na kara karuwa, yayin da hukumomi ke kara sanya dokar hana zirga-zirga a jihohi daban-daban na kasar.

18:10 Mun kawo karshen bayanan da muke kawo muku kai tsaye game da abubuwan da suka faru a rana ta uku ta yajin aikin gama-gari da zanga-zanga da kungiyoyin kwadago suka kira domin nuna adawa da janye tallafin man fetur. Mun gode da gudummawar da kuke bamu, sai a ci gaba da kasancewa da sashin Hausa na BBC.

17:53Hotuna: Dubban mutane sun fito zanga-zanga a rana ta uku ta yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya. http://www.bbc.co.uk/hausa/multimedia/2012/01/120111_nigeriaday3_gallery.shtml

16:34 Rahotanni daga Najeriya na nuna cewa adadin jama'ar da suka fito kan tituna domin zanga-zangar adawa da janye tallafin mai na kara karuwa, yayin da hukumomi ke kara sanya dokar hana zirga-zirga a jihohi daban-daban na kasar.

15:35A Abuja babban birnin Najeriya wasu duruwan matasa da suka yi zaman dirshen a gudummuwar Wuse sun zargi jami'an tsaro da abka musu cikin dare inda suka yi musu dukan tsiya tare da raunata wasu daga cikinsu kamar yadda daya daga cikin matasan ya shaida wa BBC. Sai dai jami'an 'yan sanda sun ce matasan ne da laifi domin kungiyar kwadago bata nemi izinin kaiwa dare ba.

15:22 Rahotanni a Najeriya sun ce wasu matasa sun kona wani gida guda daya, kana suka rushe masallacin da ke kusa da shi a garin Obolloafor na yankin karamar hukumar Udenu ta jihar Enugu. Ba a yi asarar rayuka ba, amma an rasa dukiya mai dimbin yawa. Sai dai hukumomin 'yan sanda sun ce, ba wai hari ne aka kai ba, gobara ce ta tashi a wajen da abin ya auku.

15:09 Domin sauraron shirin rana na sashin Hausa na BBC kai tsaye latsa wannan rariyar likau din http://www.bbc.co.uk/hausa/audio_console.shtml?programme=hausalatest

15:06 Gwamnatin jihar Naija ta kafa dokar hana zirga-zirga ta sa'o'i 24 a dukkan sassan jihar, biyo bayan tarzomar da aka yi wadda ta kai ga kona gidaje da ofisoshin gwamnati da na siyasa da dama lokacin wata zanga-zanga da daruruwan jama'a suka gudanar a game da batun cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarrayyar Najeriya ta yi.

14:43 "Kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram a arewacin Najeriya, ta fitar da wani faifan vidiyo ta hanyar sadarwa ta Internet inda ta ke kare hare-haren da ta kaiwa mabiya addinin Krista a baya-bayan nan a kasar. Malam Abubakar Shekau, wanda aka ce a yanzu shi ne shugaban Boko Haram din, ya ce, sun kai hare-haren ne domin daukar fansar kisan da aka yiwa Musulmi a arewacin Najeriyar.Abubakar Shekau ya ce, jami'an tsaron Najeriya ba za su razana kungiyarsa ta Boko Haram ba".

14:32 A jihar Kaduna jama'ar jihar ne ke nuna damuwa a bisa dokar hana fita ta sa'o'i 24 da aka kafa a jihar sanadiyyar zanga-zangar kyamar cire tallafin mai data so ta kazance a jiya. Wasu jama'ar jihar sun shaida wa BBC cewa a yanzu sun takura matuka sanadiyyar yajin aikin da kuma dokar ta hana fita. Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ba ta yi hakan ne don takura al'umma ba, sai don kare barkewar mummunan rikici.

14:12"Wakilin BBC a jihar Legas Umar Shehu Elleman, ya ce an kashe dan sanda daya da wani mai zanga-zanga a unguwar Obalende ta jihar ta Legas".

13:52 "Rahotannin da ke fitowa daga kasar Ghana sun ce a jiya da maraice ne 'yan sanda a birnin Accra suka cafke wata motar daukar kaya makare da dimbin bindigogi da harsasai a kan hanyarta ta zuwa Najeriya. 'Yan sandan sun kuma ce sun kama wasu 'yan Najeriya guda biyu daya daga jihar Anambra daya kuma daga jihar Ogun da kuma 'yan Ghana guda uku da ke cikin motar. Babbar Kwamandar 'yan sandan da ke kula da jihar Accra wato DCOP Rose Atingah Bio wadda bata bayyana adadin bindigogi da harsasan ba, ta ce suna da yawa sosai kuma suna ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin".

13:43 Rahotanni daga jihar Naija na cewa an samu tashin hankali a wasu sassan jihar, inda wasu mutane suka farfasa wasu gine-ginen gwamnati tare da toshe manyan hanyoyi. Wata majiya a jihar ta shaida wa BBC cewa "an kashe dan sanda daya a tashin hankalin, wanda ya barke lokacin da jama'a ke zanga-zangar adawa da janye tallafin man fetur".

13:03 "Mun dora alhakin abinda ya faru kan wasu 'yan siyasa da suka fadi a zaben da ya gabata, kuma suka sha kashi a kotu. Suna amfani da zanga-zangar 'yan kwadago domin haifar da rikicin siyasa a kasar", kamar yadda sanarwar jam'iyyar PDP ta bayyana.

12:46 Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta yi Allah wadai da tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan yajin aiki da zanga-zangar da ake yi a kasar wacce kungiyoyin kwadago da na farar hula suka shirya.

12:10 Wakilinmu a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai, ya ce jama'a sun fito babu masakar tsinke a jihar, inda suke yin kalaman Allah wadai da matakin gwamnatin kasar na janye tallafin man fetur. Zanga-zangar na tafiya lami-lafiya. Akalla mutane biyar aka kashe a ranar farko ta zanga-zangar.

11:55 A sakon da ya aiko mana daga jihar Jigawa Ibrahim Sule cewa yayi: "Kai Allah ya karemu yau kasuwar Gumel amma kamar anyi ruwa an dauke".

11:49 "Wannan zanga-zanga tare da yajin aiki na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar rikice-rikicen addini da na kabilanci - ko a ranar Talata mutane 13 sun rasa rayukansu a wasu hare-hare da aka kai kan wani masallaci a jihar Edo da kuma wata mashaya a garin Potiskum".

11:43 Rahotanni daga Legas na cewa masu zanga-zanga sun toshe wata babbar hanya da ta take kaiwa cikin birnin inda yawancin masu hannu-da-shuni ke zaune. Godwin Bassey, daya daga cikin masu zanga-zanga ya shaida wa kamfanin dillancin Labarai na Associated Press cewa " A shirye muke da abinda duk zai faru. Za mu iya kwana anan har san biya mana bukatarmu".

10:56 Hadaddiyar Kungiyar Kwadago ta kasa reshen Jihar Ribas dake Kudu maso Kudancin Najeriya ta bada umarnin rufe duk rijiyoyin mai dake Jihar Ribas tun daga ranar Laraba.Tattalin arzikin Najeriyar dai ya dogara ne kacokan akan albarkatun man Fetur sabanin yadda yake bayan samun 'yancin kan kasar.

10:37 "Gwamnatin Najeriya ta yi gargadin cewa duk wani ma'aikaci da ya ci gaba da shiga yajin aikin da kungiyar kwadago ta kira, ba za a biya shi albashi ba".

10:19 An shiga rana ta uku ta yajin aikin gama-gari da kungiyoyin kwadago suka kira a Najeriya domin nuna rashin amincewa da matakin gwamnati na janye tallafin man fetur.

Karin bayani