Amurka za ta binciki faifen bidiyo sojojinta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sojojin ruwa na musamman na Sintiri a Afganistan

Rundunar Sojin Amurka ta ce tana binciken wani faifen bidiyo da ke nuna wasu sojinta hudu na musamman ke fitsari a kan wasu gawawwakin mayakan Taliban a Afghanistan.

A cikin wata sanarwa da rudunar sojojin ruwa ta musamman ta fitar na kasar, ta ce har yanzu ba ta tantance inda bidiyon ya fito ba da kuma sahihancinsa.

Amma rundunar ta ce tana aiki ne domin gano mutane da ke cikin hoton bidiyon.

Wani mai magana da yawun Hukumar tsaro ta Pentagon ya bayyana faifen bidiyon a matsayin wani abu mai matukar damuwa a yayinda ya ce Amurka ba za ta taba amincewa da irin dabi'ar da aka nuna sojojinta ke yi ba.

Wata Kungiyar addinin Islama a Amurka wadda ake kira Council on Islamic-American Relations, ta yi tur da bidiyon.

Mai magana da yawun Kungiyar, Ibrahim Hooper ya tabbatarwa BBC, sahihancin bidiyon amma bai dai iya tantance lokacin da aka dauki hoton ba, kuma aka sanya a shafin Intanet.

Idan har aka tabbatar da sahihancin bidiyon zai kara harzuka jama'a a fadin duniya, ganin irin hotunan da aka fito da su a shekarun baya, wadanda su ka nuna sojojin Amurka na ci zarafin wasu fursononi a gidan kaso na Abu Ghairab dake Afghanistan.

Rudunar sojin ruwa na musamman a Amurka dai ta ce idan har ta kammala binciken ta kuma ta tabbatar da sahihancin bidiyo, za ta hukunta duk wani wanda ke da hannu a aika-aikar.

Karin bayani