Burma ta cimma yarjejeniya da 'yan tawayen Karen

Hakkin mallakar hoto AP

Hukumomi a Burma sun sa hannu a kan wata yarjejeniyar tsagaita wuta da 'yan tawayen kabilar Karen.

Abunda ake ganin zai kawo karshen karshen yakin basasar da ya fi ko wanne dadewa a duniya.

Wata tawagar gwamnati da hafsoshin sojan kasar ce dai ta gana da kusoshin kungiyar 'yan tawayen ta Karen National Union a babban birnin Jihar Karen.

Jagoran tawagar gwamnatin, Min Aung, ya ce wannan matakin farko ne, inda suka cimma yarjejeniyar da za ta baiwa 'yan tawayen damar bude ofishi a babban birnin kasar kuma su rika yawo a ko ina cikin kasar ba tare da tsangwama ba.