Al'amura sun tsaya cik a Najeriya

Nigeria
Image caption Dudun dubatar jama'a ne ke fita kan tituna a kullum tun fara yajin aikin

Yajin aikin kasa baki daya a Najeriya ya tsayar da al'amura cik a kasar inda dubun dubatar jama'a ke fita kan tituna domin nuna adawa da matakin gwamnati na janye tallafin man fetur.

Kungiyoyin ma'aikatan hakar mai sun yi barazanar rufe tashoshin hako danyan mai na kasar.

Asibitoci da makarantu da bankuna da shaguna da wasu kasuwanni da gidajen mai sun kasance a rufe.

Yajin aiki da zanga-zanga sun kara jefa gwamnatin kasar cikin matsin lamba ganin yadda take kokarin shawo kan matsalar rashin tsaro.

Akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon tashin hankalin da ke d alaka da zanga-zanga kan man fetur.

Matsalar tsaro

Rahotanni sun ce akalla 'yan sanda biyu aka kashe a ranar Laraba lokacin da wasu gungun mutane suka mamaye tsakiyar birnin Minna, suna kona ofisoshin siyasa abinda ya sa gwamnati kafa dokar hana fita kwata-kwata.

Hare-hare kan Kiristoci a Arewacin kasar da kuma kan Musulmai a Kudanci, sun kara haifar da zaman dar-dar a zukatan jama'a.

Wannan ya sa wasu na hasashen kasar ka iya fadawa cikin yakin basasa.

An samu barkewar sabon tashin hankali a yankin Arewa maso Gabashin kasar, inda wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kashe mutane hudu a wajen garin Potiskum.

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption An samu tashin hankali a wasu sassan kasar da dama

Hukumomi sun kafa dokar fita da dare a jihar Yobe inda Potiskum din take.

A birnin Legas mafi girma a kasar, kusan mutane 10,000 ne suka fita kan tituna domin zanga-zangar lumana kan cire tallafin man fetur.

'kuma zan ci gaba'

Sai dai an samu hargisti a wasu sassan birnin, inda matasa suke kona tayoyi da muzgunawa masu kaiwa da komowa.

"Tun ranar Litinin na shiga wannan zanga-zangar kuma zan ci gaba har sai gwamnati ta mayar da farashin mai naira 65 kan kowacce lita," a cewar Dele Olaniyi, wani mai tuka motar tasi.

Mambobin majalisar wakilai da na dattawa na kokarin shiga tsakani domin shawo kan matsalar, amma babu wata nasara da aka samu kawo yanzu.

Jami'an kungiyar kwadago sun ce ba za su janye yajin aikin da suke yi ba har sai shugaba Jonathan ya janye matakin da ya dauka na kara farashin man - wanda yawancin 'yan kasar ke ganin shi ne kawai abinda suke amfana daga gwamnati.

Jonathan na fuskantar matsin lamba

Jami'an gwamnati da masana tattalin arziki sun ce janye tallafin zai samarwa da gwamnati dala biliyan 8 a kowacce shekara domin gudanar da ayyukan ci gaban kasa.

Shugaban babban bankin kasar Sanusi Lamido Sanusi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa kasar na yin asarar naira biliyan 100 a kowacce rana sakamakon yajin aikin da 'yan kwadagon suke yi.

Rikicin addini da na kabilanci a sassan kasar da dama ya kara cakuda al'amura a kasar da ke da yawan mabiya addinin Musuluci da kuma na Kirista.

Shugaba Goodluck Jonathan na fuskantar matsin lamba daga fuskoki daban-daban domin ya shawo kan halin da kasar ta samu kanta a ciki.

Masana na hasashen idan har ba a dauki wani mataki cikin gaggawa ba, to al'amura za su iya fin karfin gwamnatin.

Tuni dai aka sanya dokar tabaci da ta hana zirga-zirga a wasu jihohin kasar da dama domin shawo kan tashin hankalin da ake alakantawa da Boko Haram ko kuma wanda ya biyo bayan zanga-zangar adawa da cire tallafin man fetur.

Karin bayani