Burma ta saki pursunonin siyasa

Pursunonin Burma Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Pursunonin Burma

Kasar Burma ta saki da dama daga cikin fitattun 'yan adawar da ake tsare da su a wani muhimmin mataki na aiwatar da sauye-sauye.

Mutane dari shida da hamsin ne dai suka samu 'yanci, ciki har da jagororin daliban da suka yi bore a shekarar 1988 da kuma malaman addinin Buddha wadanda suka jagoranci jerin zanga-zanga a shekarar 2007.

Mutane da dama ne dai suka taru a kofar babban gidan yari na birnin Rangoon suna rera wakoki yayin da 'yan adawar ke fitowa.

Jagoran kungiyar 'yan kabilar Shan, Khun Tun Oo, yana cikin wadanda aka sako.

Inda ya ce bai kamata a kama shi ba tunda bai aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa ba.

Babbar jam'iyyar adawa ta kasar ta Burma, wadda Aung San Suu Kyi ke jagoranta, ta yi marhabin da sakin fursunonin tana mai cewa hakan Laraba ce mai nuni da kyakkyawar Juma'ar da za ta biyo baya.

Kungiyar Kare Hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ma ta bayyana matakin da cewa ci gaba ne mai matukar muhimmanci; sai dai kuma ta yi gargadin cewa har yanzu akwai fursunonin siyasar da ba a san adadinsu ba a tsare.

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatin ta kyale masu sa-ido na kasa-da-kasa su shiga gidajen yarin kasar.

Wani da ke tsare a da ya ce wadanda aka saki ba su da tabbacin cewa ba za a sake kama su ba a ko wanne lokaci.

Karin bayani