An soki kamfanin auna tattalin arzikin kasashe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Olli Rehn

Kwamishinan kula da harkokin tattalin arzikin Tarayyar Turai, Olli Rehn, ya soki matakin da kamfanin Standard and Poor's ya dauka na rage matsayin iya biyan bashin kasashe tara da ke amfani da kudin euro.

Kasashen da kamfanin ya rage karfin iya biyan bashin su sun hada da Faransa, da Australia, da Portugal, da Spain da sauransu.

Kamfanin ya ce ya dauki matakin ne saboda gazawar gwamnatocin kasashen wajen fitar da ingantacciyar hanyar da za ta magance tabarbarewar tattalin arzikin da suke ciki.

Sai dai Mr Rehn ya bayyana matakin da cewa bai yi dace ba.

Wani dan kasar Spain ma ya ce kamfanin ya sanya son-rai wajen daukar matakin:

''Kamfanin na da wata boyayyiyar manufa game da yadda yake auna karfin iya biyan bashin kasashe.Don haka bai kamata a amince da shi ba.Ya kamata a rika amfani da matakan da kowacce kasa ke dauka wajen magance tatarbarewar tattalin arzikinta, ba wai dogaro ga irin wadannan kamfanoni ba''.

Karin bayani