An dakatar da zanga zanga a Najeriya

Masu zanga zanga a Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga zanga a Najeriya

A Nigeria kungiyar Kwadagon kasar, watau NLC ta bada sanarwar cewa zata dakatar da zanga zangar da aka shafe kwanaki biyar ana yi a fadin kasar a ranakun asaabar da lahadi dn yin hutu da addu'o'i.

Hakan dai ya biyo bayan shawarwarin da aka fara ne jiya tsakanin gwamnatin kasar da shugabannin kungiyar kwadagon.

Kungiyar kwadagon ta ce a zaman na jiya, sun kasa jitiwu da gwamnatin kasar saboda tayin da gwamnati ta yi mata bai kwanta mata ba.

Kungiyar kwadagon ta ce, gwamnati ta nemi a maida farashin litar man fetur a kan naira dari daya da ashirin, amma ta ki amincewa da hakan, inda ta nemi gwamnatin da ta dawo da tsohon farashin naira sittin da biyar, nan da lokacin da za su daidaita da juna.

Sai dai gwamnatin ta ki karbar wannan tayin.

Karin bayani