An kasa cimma matsaya tsakanin gwamnati da NLC

jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

A Najeriya, Gwamnatin kasar da kungiyar kwadago sun kammala zama ba tare da cimma wata matsaya ba.

An shafe sai'o a ranar Alhamis ana ganawa a fadar shugaban kasar akan batun na janye tallafin man fetur inda shugaba Jonathan ya jagoranci bangaren gwamnati ciki hadda mataimakinsa da wasu gwamnoni da kuma ministoci a yayinda shugaban NLC, Comrade Abdukwaheed Umar ya jagoranci bangaren kungiyoyin kwadago.

Sai dai dukkan bangarorin biyu sun bayyana cewa sun yi tattaunawa mai fa'ida, kuma za su ci gaba da ganawa gobe Asabar.

Wannan ganawardai itace ta farko ido da ido shugaba Jonathan da 'yan kwadagon tun bayan da shugaban ya janye tallafin man fetur a ranar daya ga wannan watan abinda ya sanya kungiyar kwadago ta soma yajin aikin sai baba ta gani.

Kungiyar ma'aikatan man fetur ta kasar ta yi barazanar toshe hanyoyin hakowa da fitar da danyan mai daga ranar Lahadi idan gwamnati bata sauya matsaya ba.

Jonathan na fuskantar matsin lamba

Jami'an gwamnati da masana tattalin arziki sun ce janye tallafin zai samarwa da gwamnati dala biliyan 8 a kowacce shekara domin gudanar da ayyukan ci gaban kasa.

Shugaban babban bankin kasar Sanusi Lamido Sanusi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa kasar na yin asarar naira biliyan 100 a kowacce rana sakamakon yajin aikin da 'yan kwadagon suke yi.

Rikicin addini da na kabilanci a sassan kasar da dama ya kara cakuda al'amura a kasar da ke da yawan mabiya addinin Musuluci da kuma na Kirista.

Shugaba Goodluck Jonathan na fuskantar matsin lamba daga fuskoki daban-daban domin ya shawo kan halin da kasar ta samu kanta a ciki.

Masana na hasashen idan har ba a dauki wani mataki cikin gaggawa ba, to al'amura za su iya fin karfin gwamnatin.

Tuni dai aka sanya dokar tabaci da ta hana zirga-zirga a wasu jihohin kasar da dama domin shawo kan tashin hankalin da ake alakantawa da Boko Haram ko kuma wanda ya biyo bayan zanga-zangar adawa da cire tallafin man fetur.

Karin bayani