An shiga wani hali a siyasar Pakistan

Majalisar Dokokin Pakistan Hakkin mallakar hoto other
Image caption Majalisar Dokokin Pakistan

Majalisar Dokoki ta Pakistan za ta kada kuri'ar amincewa ko akasin haka a kan shugabancin siyasa da ma tsarin majalisar dokokin kasar ranar Litinin.

Labarin hakan ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Asif Ali Zardari ya koma kasar bayan 'yar gajeruwar tafiyar da ya yi zuwa Dubai.

Tafiyar da ya yi ranar Alhamis ta haifar da rade-radi a kafafen yada labarai saboda ta zo ne a daidai lokacin da dangantaka ke kara tsami tsakanin gwamnatinsa da rundunar sojin kasar mai karfin gaske.

Ana kuma sa ran cewa a ranar Litinin din Kotun Kolin kasar za ta saurari bahasi a wata shari'a da ta danganci zargin Shugaba Zardarin da wasu mutane da cin hanci da rashawa.

Karin bayani