'Yan sanda sun kai samame a Turkiyya

Jami'an leken asirin Turkiyya bayan samamen da suka kai Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an leken asirin Turkiyya bayan samamen da suka kai

'Yan sandan Turkiyya sun kai samame a kan daruruwan gidaje da ofisoshi a birane goma sha bakwai, sun kuma kama akalla mutane talatin da biyu.

Samamen dai wani bangare ne na matakin da hukumomin Turkiyyar ke dauka na murkushe magoya bayan kungiyar 'yan aware ta Kurdawa, PKK.

A shekara guda da ta gabata an kama daruruwan fararen hula an kuma tsare su a karkashin dokokin yaki da ta'addanci.

Sun hada da 'yan jarida da masu fafutikar kare Hakkin BilAdama da kuma lawyoyi.

Karin bayani