China ta soki gwamnatin Amurka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban China, Hu Jintao

China ta soki matakin da Amurka ta dauka na sakawa wani kamfanin kasarta takunkumi saboda ya sayarwa Iran tataccen man fetur.

Ma'aikatar harkokin wajen China ta ce matakin da Amurka ta dauka bai dace ba kuma bai yi daidai da kudurin Majalisar Dinkin Duniya kan shirin nukiliyar Iran ba.

Kamfanin na Zhuhai Zhenrong Corporation mallakin gwamnati China na daga cikin kamfanonin makamashi guda uku da Amurka ta hukunta a ranar Jumu'a saboda alakarsu da Iran.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce kamfanin na China na daga cikin wadanda suke samarwa Iran tataccen man fetur.