Tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan kwadago ta cije

Image caption Masu zanga-zangar adawa da janye tallafin man fetur a Najeriya

A Najeriya, tattaunawar da aka yi ranar Asabar tsakanin gwamnati da 'yan kwadago dangane da janye tallafin man fetur ta cije bayan da bangarorin biyu suka gaza cimma matsaya.

Gwamnatin dai ta sanar da cire tallafin man fetur ne ranar daya da watan Janairu, lamarin da ya sa farashinsa ya nunka fiye da sau biyu, abin da sa ake gudanar da yajin-aiki da zanga-zanga a duk fadin kasar.

Sai dai bayan tattaunawar da suka gudanar a daren ranar Asabar, shugaban kungiyar kwadago, Abdulwaheed Omar, ya shaidawa manema labarai cewa har yanzu ba su cimma matsaya ba dangane da yiwuwar dawo da farashin man zuwa farashin sa na baya, watau lita daya akan N65.

Ya ce:''Bamu cimma matsaya ba.Burinmu shi ne gwamnati ta dawo da farashin man fetur kamar yadda yake a baya, kafin mu janye yajin-aikin da muke yi.Daga nan mu fara sabuwar tattaunawa dangane da batun''.

A baya dai ma'aikatan da ke hakar man fetur a kasar sun yi barazanar dakatar da hakarsa idan gwamnati ba ta dawo da farashin man kamar yadda yake a baya ba.

Sai dai shugaban kungiyar kwadagon ya ce sun janye barazanar saboda su ci gaba da tattaunawa da gwamnati a kan batun.

Karin bayani