An kai hari kan mabiya Shia a Iraqi

Mabiya Shi'a a Iraqi Hakkin mallakar hoto l
Image caption Mabiya Shi'a a Iraqi

Hukumomin Iraki sun ce akalla mutane 50 sun hallaka, bayan da wani dan kunar bakin wake ya kai a kan masu ibada na 'yan Shia a birnin Basra na kudancin kasar.

Wasu karin fiye da dari sun samu raunika. 7 daga cikin mamatan , jami'an tsaro ne, wadanda ke bincika ababen hawa a wurin da abun ya faru.

Masu ibadar suna kan hanyar su ce ta zuwa wani babban massalaci na 'yan Shia dake wajen birnin na Basra, bayan sun kammala Arba'in, daya daga cikin ranaku masu tsarki ga 'yan Shia.

Wakilin BBC ya ce wadanda suka shaida al'ammarin sun ce dan kunar bakin waken ya janyo masu ibadar ne a jika, yana nuna cewa yana rarraba masu abinci ne da ruwan sha, kafin ya tada nakiyoyin dake jikinsa.

Wannan tashin hankali dai ya zo a daidai lokacin da ake samun karuwar zullumi tsakanin 'yan Shia masu rinjaye a Irakin da kuma 'yan Sunni.

Karin bayani