Za a tattauna kan janye tallafin mai a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga-zanga game da janye tallafin man fetur a Najeriya

A ranar Asabar ce ake sa ran gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da tattaunawa da kungiyoyin kwadago don yiwuwar kawo karshen yajin aiki da zanga-zangar da ake yi a kasar sakamakon janye tallafin man fetur da gwamnatin ta yi.

Bangarori biyun dai sun yi zama a ranar Alhamis da ta gabata ba tare da cimma wata matsaya ba.

Kungiyar kwadagon ta ce sun kasa jitiwu da gwamnatin kasar ne saboda tayin da gwamnati ta yi mata bai kwanta mata ba.

Ta ce gwamnati ta nemi a mayar da farashin litar man fetur a kan naira dari daya da ashirin, amma ta ki amincewa da hakan, inda ta nemi gwamnatin da ta dawo da tsohon farashin naira sittin da biyar, nan da lokacin da za su daidaita da juna.

Sai dai gwamnatin ta ki karbar wannan tayin.

Harkoki da dama sun tsaya a Najeriyar sakamakon yajin aikin, koda yake kungiyar kwadagon ta dakatar da zanga-zangar zuwa gobe Lahadi, lokacin da ake sa ran za su kammala tattaunawa da gwamnati.