Ana zargin JTF da muzgunawa jama'a a Maiduguri

Jami'an tsaro a Maiduguri
Image caption Jami'an tsaro a Maiduguri

Al'ummar birnin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya suna ci gaba da kokawa da yadda suka ce jami'an rundunar tsaro ta JTF wadda aka dankawa alhakin tabbatar da zaman lafiya a Jihar ke musguna musu.

Rahotanni sun zargi jami'an tsaron ne da bi layi-layi suna dukan mutane da wukaken d ke kan bindigoinsu jiya Juma'a.

An kuma ba da rahoton cewa an fasa wasu shaguna cikin daren jiya duk kuwa da dokar hana fitar da aka kafa daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe.

Sai dai yunkurin jin ta-bakin rundunar bai yi nasara ba.

Karin bayani