Ba gudu ba ja da baya! Inji NLC

Masu zanga zanga a Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga zanga a Najeriya

A Najeriya yanzu haka gwamnatin kasar a karkashin jagorancin shugaba Goodluck Jonathan na can na ganawa da shugabannin kungiyoyin kwadago na kasar, da nufin cimma matsaya dangane da janye tallafin man fetur da gwamnatin ta yi.

Abin da ya sa aka kara farashin man daga naira 65 zuwa 141.

Wannan dai ya sa jama'a a sassa daban daban na kasar shiga yajin aiki tare da yin zanga zanga, domin neman gwamnatin da ta dawo da farashin man kamar yadda ya yake a da.

A ganawar da sukai gabanin taronsu da gwamnatin Najeriyar, shugabannin kwadagon dai sun ce baza su yadda da komai ba har sai gwamnatin ta dawo da tsohon farashin man fetur din na naira 65, alabashshi sai a tattauna kan yadda za'a janye tallafin.

Karin bayani