Qatar na san a tura dakarun soji Syria

Sarkin Qatar, Sheikh Hamad bin Khalifa al-Thani Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sarkin Qatar, Sheikh Hamad bin Khalifa al-Thani

Sarkin Qatar, ya ce ya kamata kasashen Larabawa su tura sojoji zuwa Syria, domin kawo karshen yadda gwamnatin kasar ke murkushe masu zanga-zangar nuna adawa da ita.

Sheikh Hamad bin Khalifa al Thani, ya yi wadannan kalamai ne yayinda yake amsa wata tambaya a kan batun daukan matakin soja a kan Syria a wata hira da wani gidan talabijin na Amurka.

Wakilin BBC ya ce zaa samu cikakken bayani a kan kiran da Sarkin na Qatar ya yi, lokacin da zaa watsa hirar da aka yi da shi a gobe dad dare.

Qatar dai tana daya daga cikin kasashen Larabawan dake kan gaba wajen sukar lamirin gwamnatin Syriar, kuma Pira ministan ta ne ke jagorantar tawagar 'yan kallo na kungiyar kasashen Larabawa dake ziyara a kasar.

Sai dai an soki lamirin tawagar bisa gazawar da ta yi na kawo karshen zubar da jini a kasar.

Karin bayani