'An hallaka fararen hula 16 a Sudan'

Mayaka a Sudan
Bayanan hoto,

Mayaka a Sudan

'Yan tawaye a jihar Kudancin Kordofan da ke Sudan sun ce sojojin kasar sun hallaka fararen hula guda 16 a cikin kwanaki biyu da suka shafe a karshen mako suna ruwan bama-bamai a yankin.

Dakarun sojin kasar sun tabbatar da cewa sun gudanar da wadansu ayyuka a yankin, amma sun musanta kashe fararen hula.

'Yan tawayen sun ce su ma sun hallaka wasu daga cikin dakarun gwamnati a musayar wutar da aka yi amma rundunar sojin ta musanta hakan.

Jihar ta Kudancin Kordofan, wadda ke da arzikin man fetur, ta kasance a karkashin ikon gwamnatin Khartoum a lokacin da Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai a watan Yulin bara, amma 'yan tawayen SPLM sun ci gaba da yaki.