An kama wani da ake zargin dan boko haram ne a Abuja

jagoran kungiyar Boko Haram a Nijeriya

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

jagoran kungiyar Boko Haram a Nijeriya

Rahotanni daga Najeriya, sun ce rundunar 'yan sandan kasar ta kama wani mutum da ake zargin dan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah Lidda'awati Wal Jihad ne da aka fi sani da Boko Haram a Abuja babban birnin kasar.

Ana dai zarginsa ne da hannu a harin bomb din da aka kai ranar kirsimeti a cocin St Theresa dake garin Madallah, a karamar hukumar Suleja na jihar Neja, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane arba'in.

Rahotannin sun nuna cewa an kama mutumin ne, da aka ce sunansa Kabiru Sakkwato ne, a gidan gwamnatin jihar Borno dake Abuja.

Jami'an tsaron Nijeriya, sun ce da ma sun dade suna bin diddigin mutumin, kafin a kai samamen na hadin gwiwa wajen kama shi.

Kamun nasa ya zo ne a daidai lokacin da jami'an tsaron Nijeriya ke ci gaba da shan suka cewar sun gaza shawo kanmatsalar tsaro da ta addabi kasar, musamman hare haren da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram da kai wa.