Aikin ceto na ci gaba a tsibirin Giglio

jirgin ruwan da ya tuntsure Hakkin mallakar hoto AP
Image caption jirgin ruwan da ya tuntsure

Ma'aikatan gabar teku a tsibirin Giglio na kasar Italiya sun ce an gano karin gawarwaki biyu a katafaren jirgin ruwan yawon bude idon nan, mai suna Costa Concordia, wanda rabinsa ya nutse.

Tun farko an bada sanarwar mutuwar mutane uku, aka kuma ce akwai wasu sha bakwai da ba a ji duriyarsu ba.

Mutane sama da dubu hudu ne ke cikin jirgin ruwan.

Ana yi ma matukin jirgin ruwan tambayoyi, bayan da aka kama shi.

Ya shaidawa gidan talabijin na Italiya cewa na'urar dake masa jagora ta nuna masa cewar, jirginm ruwan na nesa da gabar tekun , don haka da wuya ya iya karo da dutse.

Karin bayani