PENGASSAN na shirin shiga yajin aiki

Image caption Masu zanga zanga a Nijeria

Kungiyar manyan ma'aikatan man fetur a Najeriya wato PENGASSAN ta ce idan har ba a sasanta ba tsakanin gwamnatin tarraya da kuma kungiyoyin kwadagon kasar wato NLC da TUC a taronsu na daren yau, to ba tada wani zabi illa ta shiga cikin yajin aikin a gobe Litinin.

Ko a jiya ma dai gwamnatin Nijeriya da bangaren 'yan kwadago sun shafe sa'o'i a fadar shugaban kasa suna tattaunawa akan batun janye tallafin man fetur, da kuma farashin man akan kowanne lita, amma sai suka kasa samun daidaito.

Janye tallafin a farkon shekarar ne ya sa farashin mai ya ninka, lamarin da ya haddasa tashin gwauron zabo na farashin kaya da kudaden sufuri da makamantansu.

Zanga zangar da aka gudanar daga ranar Litinin zuwa ranar Juma'a sun sa al'amurra sun tsaya a cik a kasar, sun kua haddasa arangama tsakanin jami'an tsaro da masu zanga zangar a sassa daban daban na Nijeriya.

Mutane akalla bakwai ne ake cewar sun mutu a sakamakon zanga zangar, bayan daruruwa da ake zargin an jikkata.

Karin bayani