Shugaba Assad ya yi afuwa a Syria

shugaba Assad Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption shugaba Assad

Shugaba Bashar al-Assad na Syria bada sanarwar yin ahuwa ga duk wadanda suka aikata laifukka akan gwamnatinsa tun daga lokacin da aka fara boren bijirewa gwamnatin a farkon bara.

Kamfanin dillacin labaran Syriar, ya ce ahuwar ta shafi wadanda suka yi zanga-zanga ta lumana da kuma wadanda suka dauki makamai ba bisa ka'ida ba.

Wannan dai ba shi karon farko da shugaba Assad din ke yin irin wannan ahuwar ba, kuma har yanzu ba a san takamaimai ko an saki wasu fursunoni a sakamakon ahuwar ba.

Wani wakilin BBC ya ce ga alama matakin ahuwar ya saba wa wani jawabi da Mr Assad din ya yi a makon jiya, inda ya zargi 'yan adawa cewa 'yan ta'adda ne, ya kuma lashi takobin murkushe su.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban ki-Moon ya kara jaddada matsayin majalisar cewa ya kamata shugaba Assad din ya daina kashe al'umar kasarsa.

Mr Ban ya bayyana hakan ne a wata ziyara da yake a Lebanon, inda ya ke nuna cewa, juyin juyahalin da ake a kaasshen arabnawa na nuna cerwar al'umar kasashen sun dawo daga rakiyar mulkin kama-karya.

Karin bayani