Gazawa wajen agazawa fari a gabashin Afrika

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kusan mutane miliyan goma ne suka kamu da matsalar yunwa a gabashin Afrika

Wani rahoto wanda biyu daga cikin manyan kungiyoyin ba da agaji na Burtaniya suka wallafa ya ce an yi asarar dubban rayuka da miliyoyin daloli ne saboda gazawa wajen mai da martanin da ya dace kuma a kan lokaci ga gargadin cewa akwai fari a gabashin Afirka.

Kungiyoyin Oxfam da Save the Children sun ce sai da aka kwashe fiye da watanni shida kafin a fara daukar mataki.

An dai samu bayanai ne daga tauraron dan-Adam da ma mutanen da suka ganewa idanuwansu cewa mai yiwuwa a fuskanci matsananciyar yunwa.

Hakan ya faru ne a cewar kungiyoyin saboda gazawar gwamnatocin Kenya da Habasha wajen yarda da girman bala'in da kuma yadda ma'aikatan agaji suka rika jin cewa a baya ma sun sha ganin matsaloli irin wannan.

Wasu kasashen ma, kin bada agaji su ka yi saboda suna neman a nuna musu shaida.

Akwai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa sama da mutane miliyan goma ne ke bukatar agajin gaggawa saboda matsanaciyar yunwa.

Daruruwan mutane ne kuma su ka rika tururuwa zuwa, sansanonin 'yan gudun hijira domin neman abinci, musamman ma a wasu sassan kasar Somalia inda gwamnati da kungiyar al-Shabab ke fafatawa.