'Kyaftin din jirgin Italiya ya bar jirgin a lokacin da ake aikin ceto'

Sautin da aka nada daga jirgin ruwan masu yawan shakatawa na kasar Italiya, wato Coster Concordia, ya nuna matukin ya bar jirgin a lokacin da ake aikin ceto mutanen da ke ciki.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jirgin ruwan Shakatawan Italiya da ya kife

A wata tattaunawa da aka yi mai zafi, an ji wani mai tsaron gabar ruwa na baiwa matukin jirgin Francesco Schettino umarnin komawa cikin jirgi ya fadi yawan pasinjojin da har wannan lokacin ke ciki. An ji mai tsaron gabar ya fadi cikin fushi cewa tilas ne Mr Schettino ya rika fada masa abinda ke faruwa ba wai akasin hakan ba.

Matukin jirgin dai na tsare a gidan yari tun lokacin da jirgin ruwan ya yi hadari, za kuma a iya tuhumarsa da laifin kisa ba da niyya ba.

Amma dai ya musanta aikata wani abu ba dai dai ba.

Sakaci

Akwai dai hasashen da jama'a da dama ke yi kan dalilan da su ka haddasa hatsarin jirgin ruwan, amma a yanzu haka za'a iya tantance taka mai mai abun da ya faru bayan an gano daya daga cikin na'urar nadan bayanai a jirgin.

Kamfanin dillancin Labarai na Italiya, (Ansa) ya ruwaito cewa, daya daga cikin na'urar da aka gano na dauke ne da wata hira da kyaftin din Jirgin yayi da wani jami'in hukumar kula da jiragen ruwa a gabar teku su ka a lokacin da jirgin ke kifewa.

Jami'in dai a hirar ya bukaci kyaftin din jirgin da ya tsara yadda za'a kwashe mutanen jirgin a yayinda yake kan nitsewa.

Jami'in ya kuma nemi kyaftin din da ya gaya masa yawan mata da yara dake jirgin amma sai ya ki.

Amma a yayinda aka samun karin bayanai kan abubuwan da suka haddasa hatsarin jirgin, akwai alamar tambaya kan kyaftin da cewa ya yi sakaci.

Karin bayani