An kama masu babura da dama a arewacin Najeriya

Image caption Taswirar Najeriya

Rahotannmi daga arewa amso gabashin Najeriya na cewa hukumomin tsaro sun kama mutane da dama a yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalar tsaro a kasar.

Bayanai dai na cewa mutanen da hukumomin tsaron suka kama tun daga makon da yagabata lokacin da aka fusknaci zanga-zangar kasa baki daya kan janye tallafin man fetur da kuma wasu hare-hare na yan bidniga da na bama-bamai a yankin arewa maso gabashin Nijeriyar suna da yawan gaske, inda kuma yanzu haka yan uwa da iyalan wadanda aka bada labarin an Kaman ke ta nuna damuwa.

Hukumomin tsaro a jihar Gombe inda aka kama dimbin mutanen dai sun bayyana cewa suna kan gudanar da bincke ne kan mutanen, wadanda rahotanni suka ce galibinsu mahaya babura ne.

Wasu daga cikin yan uwan wadanda aka kama dai sun bayyana cewa wadanda aka Kaman na kan hanyarsu ce ta tserewa daga tashin hankali amma sai hukumomin tsaron suka kama kana suka tsare su tsawon kwanaki, kamar yadda Malam Sani Sabo wani mazaunin garin Gombe wanda ya ce akwai biyu daga cikin yan uwansa da aka kama kuma kawo yanzu ba a sake su ba.

Damuwa

Shi Abdullahi Umar Bakunawa, dake jihar Bauchi, ya nuna damuwa kan kama wasu daga cikin yan uwansa da aka kama a jihar ta Gombe a akan hanyarsu ta komawa gida domin tsere wa zaman dar-dar a yankin.

To sai dai kuma da na tuntubi kakakin rundunar yansandan jihar Gombe, ASP Ahmed Kidaya Muhammad, ya tabbatar mani da cewa sun kakkama mutane da asuke zargi, amma kuma bayan da sukam gudanar da bincike, sun saki wadanda basa da wasu alamu na alamu na lafi, yayin da suke ci gaba da bincike kan wadabnda ke hannunsu.

Kakakkin na rundnar yansanda, ya kara da cewa duk wanda ke ikirarin cewa an kama dan uwansa to ta je ga run dundunar domin a bincika da nufin gano gaskiyar al'amari sai dai kuma y ace ba zai iya gaya mani adadin mutanen da suka kama ba.

A baya-bayan nan an fuskanci hare-haren yan bindiga da na bama-bama a Nijeriya musamman a yankin araewa maso gab asjhin kasar, baya ga zanga-zangar kasa baki daya inda hukumomi suka tsaura matakan tsaro da kuma bincike da nufin farauta masu aika-aikar.