Fira Ministan Pakistan ya kare Shugaban kasar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Pira Ministan Pakistan, Yusuf Raza Gilani

Firayim Ministan Pakistan Yusuf Raza Gilani ya kare shawararsa ta kin neman hukumonin Switzerland su ci gaba da binciken zargin Shugaba Asif Ali Zardari da cin hanci da rashawa.

Mista Gilani ya shaidawa kotun kolin kasar cewa Shugaba Zardari na da kariya daga tuhuma kuma ci gaba da irin wannan bincike a kan zababben shugaba ba zai zama alheri ba.

An dage ci gaba da sauraron bahasi a tuhumar Mista Gilani da raina umurnin kotu zuwa ranar uku ga watan Fabrairu.

Pakistan din dai na fama ne da takaddamar siyasar da ke barazanar kawo karshen gwamnatin Mista Gilani.

Bayyanar Pira Ministan Pakistan Yusuf Razaka Gilani a gaban kotun kolin kasar, wata takkadama ce ta baya baya nan ta siyasa da ta kunno kai, wadda ta hada da gwamnatin kasar da bangaren shari'a da kuma Sojojin kasar.

Shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zadari na cikin 'yan siyasar kasar da hukumomi a Switzerland ke tuhumar su da cin hanci.

Karin bayani