An murkushe 'yunkurin juyin mulki' a Bangladesh

Janar Muhamad Mas'ud Razzaq Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Janar Muhamad Mas'ud Razzaq

Rundunar sojojin kasar Bangladesh, ta ce ta murkushe wani yunkuri da wasu Jami'an sojoji da ke bore suka yi na hambarar da Priyi Ministar Kasar Sheikh Hasina.

Wani kakakin rundunar sojojin, Janar Muhamad Mas'ud Razzaq, ya ce gungun wasu masu kaifin ra'ayin addini ne ke da alhakin wannan makarkashiyar.

Yace tuni aka gano wasu daga cikinsu, kuma za'a gurfanar da su a gaban kotun soji ta Bangladesh din.

Waklin BBC, ya ce sai dai kakakin rundunar sojan ya ce wadanda suka shirya wannan abu ba su da yawa.

Ya kuma kara da cewa kakakin rundunar sojojin ya tsaya kai da fata akan cewar wasu kalilan ne suka kitsa wannan abu, kuma tuni an gano ko su wanene.

Shi ma Shahinul Islam, kakakin ma'aikatun tsaro na kasar, ya ce dama gwamnati ta san da zamansu.

Karin bayani