Kamfanin Kodak ya tsiyace

George Eastman wanda ya kirkiro da kamfanin Kodak Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption George Eastman wanda ya kirkiro da kamfanin Kodak

Kampanin Amurkar nan mai yin kyamarorin daukar hoto da ma fina-finan daukar hoton Easman Kodak, ya gabatar da takardun cewa ya tsiya ce.

Kampanin Kodak ne ya kirkiro kyamar daukar hoto ta hannu, ya kuma taka rawa wajen ganin mutane masu karamin karfi sun amfana daga fasahar ta daukar hoto.

A shekarun 1880 ne wani mutum mai suna George Eastman ya kafa kampanin na Kodak, wanda kuma yan kasance daya daga cikin mafiya shahara a duniya a fannin daukar hoto.

Kamarar ta Kodak da ita aka dauki hoton mutum na farko da ya sauka a duniyar wata.

Sai dai kamfanin ya yi sanyin jiki wajen tafiya da zamani musamman sauye-sauye a fasahar kirkire-kirkire abinda ya sa darajarsa ta yi ta faduwa a cikin shekaru 15 da suka gabata.

Wani wakilin BBC ya ce, kamfanin na Kodak na fatan farfadowa daga tsiyacewar da ya yi a shekarar 2013, hakan zai ba shi damar ci gaba da gudanar da harkokinsa da kudaden da suka kai dala miliyan dari tara da zai samo daga bankin Citigroup na Amurka.