Sojojin NATO 6 sun mutu a hadarin jirgin sama a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Helifkwatar rudunar tsaro ta NATO

Sojojin kungiyar tsaro ta NATO su shida sun mutu a wani hadarin jirgin sama mai saukar ungulu a kudancin Afghanistan.

Har yanzu dai ba a san kasashen da mamatan suka fito ba.

Wani mai magana da yawun sojojin ya ce ana binciken musabbabin hadarin.

Ya ce ba rahotannin da ke nuna cewa akwai masu ta da kayar a yankin lokacin da al'amarin ya auku.

A watan Agustan da ya gabata ma sojoji talatin, akasarinsu daga runduna ta musamman ta sojin ruwan Amurka, sun mutu lokacin da helikwaftan da suke ciki ya rikito a gabashin Afghanistan.