An kashe dakarun Faransa a Afghanistan

Dakarun Faransa a Afghanistan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ba wannan ne karon farko da aka kashe dakarun Faransa a Afghanistan ba

Shugaban kasar Faransa Nicolaz Sarkozy, ya dakatar da duk wani horo da aikin da suke tare da dakarun sojin Afghanistan, bayan da wani sojan Afganistan din ya kashe dakarun sojin Faransar hudu.

Wasu karin sojojin Faransar 8 ne suka jikkata a harin da aka kai a Gundumar Kapisa.

A cewar jami'an Afghanistan, lamarin ya afku ne a yankin Tagab mai fama da rikici - inda dakarun Faransa da na Afghanistan suke gudanar da ayyuka tare.

Jami'an tsaron Afghanistan biyu da kuma dakarun sojin kasa-da-kasa karkashin jagorancin Nato, sun tabbatar da afkuwar lamarin, sannan suka ce an tsare sojin da ake zargi da kai harin, sai dai basu bayar da wani karin bayani ba.

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya yi kakkausar suka ga harin, inda ya ce dakarun Faransa sun je Afghanistan ne domin su taimakawa abokan huldarsu.

"Faransa ba za ta taba amincewa wadanda take aiki tare da su su kashe koda daya daga cikin sojojinta ba.

"Sojojin Faransa ba sun je Afghanistan ba ne domin dakarun kasar su kashe su. A don haka na yanke shawarar tura ministan tsaro da kuma babban hafsan sojojinmu nan take zuwa kasar, a cewarsa.

"Kafin nan kuwa, duka harkokin horo da na taimakon soji da dakarun Faransa ke yi an dakatar da su".

Mr Sakozy bai tsaya anan ba, domin kuwa ya ce yana duba yiwuwar janye sojojin kasar daga Afghanistan da wuri kafin lokacin da aka tsara:

"Mu kawayen Afghanistan ne," a cewarsa. "Amma ba zan amince sojojin kasar su rinka bude wuta kan sojojinmu ba. Idan babu wani tsari na inganta tsaro, to akwai yiwuwar mu janye dakarunmu".

Shugaba Sarkozy ya ce rahoton da ministan tsaron kasar Gerrard Longuet zai gabatar shi ne zai share fagen matakin da kasar za ta dauka.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Faransa ke rasa dakarunta a gundumar Kapisa ba, ko a watan Yulin bara, sai da wasu sojinta biyar suka rasa rayukansu sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai musu lokacin da suke sunturi.

Karin bayani