Mai yiwuwa Amurka ta rufe ofishinta a Syria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sakatariyar Wajen Amurka, Hillary Clinton

Jami'ai a birnin Washington sun ce Amurka na duba yiwuwar rufe ofishin jakadancinta a Syria saboda damuwar da take nunawa akan sha'anin tsaron kasar.

Jami'an sun ce suna magana da hukumomin Syria da ma gwamnatocin kasashen Burtaniya da kuma China, wadanda su ma ke da ofisoshin jakadanci a Syria.

Amma har yanzu ba a yanke shawara ta karshe game da batun ba.

An dai kashe sama da mutane dubu biyar, an kuma jikkata wadansu mutanen da dama a Syria tun lokacin da aka soma zanga- zangar nuna kin jinin gwamnati a watan Maris.

Ba da dadewa ba ne wata tawagar kungiyar kasashen Larabawa ta kammala aikin sa-ido a Syria, amma ta gaza wajen kawo karshen rikicin.