Burtaniya za ta kara yawan tallafin da take bayarwa

Image caption Firayim Ministan Burtaniya, David Cameron

Gwamnatin Burtaniya za ta kara yawan tallafin da take bayarwa wajen yaki da cututtuka irinsu zazzabin cizon sauro.

Gwamnatin Burtaniyan ta yi alkawarin bayar da dala miliyan 380 cikin shekaru hudu masu zuwa, gabanin wani babban taro da shahararren dan kasuwar Amurkan nan, Bill Gates, zai karbi bakwanci.

Taron dai wani bangare ne na jawo hankalin kasashen duniya domin yaki da wasu cututtuka irin su HIV da malariya da ke hallaka mutane fiye da dubu dari biyar a kowacce shekara.

Mutane biliyan daya ne ke kamuwa da irin wadannan cututtuka da akai watsi da su, kuma fiye da mutane dubu dari biyar ne ke mutuwa sakamakon kamuwa da cututtukan.