Jam'iyyun Islama sun lashe zaben Masar

Wasu jami'an zabe a Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu jami'an zabe a Masar

Sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin Masar da aka gudanar a matakai uku, ya tabbatar cewa jam'iyyun Islama ne suka yi nasara da gagarumin rinjaye.

Hukumar zaben kasar ta ce Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood ta lashe kashi 38 cikin 100 na kujerun da aka waarewa jam'iyyun siyasa, wanda shi ne kusan kashi 50 cikin 100 na kuru'un da aka kada.

Haka ita ma jam'iyyar Nour ta samu kashi kusan kashi 25 cikin 100 na kuru'un da aka kada, wanda ya nuna cewa jam'iyyun Islama sun lashe kusan kashi 2 cikin 3 na kujerun da ake da su a majalisar dokokin Masara din.

Zaben dai, wanda aka gudanar a cikin sama da watanni biyu, shi ne na farko da ake yi a kasar tun bayan da aka kifar da gwamnatin shugaba Mubarak, sakamakon boren da jama'ar kasar suka yi a bara.

Karin bayani