An sanya dokar hana-fita a Kano

Image caption Wani gida da harin bama-bamai ya shafa a Kano

Hukumomin Najeria sun kafa dokar hana fita ta awanni 24 a jahar Kano da ke arewacin Kasar, bayan wasu hare-hare da aka kai da bama- bamai sun kashe akalla mutane shida a birnin.

Ganau sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya kutsa kai cikin hedikwatar 'yan sandan jahar, inda kuma wasu jerin fashewar bama- baman suka biyo baya a wasu ofisoshin 'yan sanda da kuma ma'aikatun gwamnati.

Wata ganau ta shaidawa Nasidi Adamu Yahya cewa ta ga mutane biyu da bama-baman suka yi kaca-kaca da su.

Kungiyar Jama'atu alhul Sunna lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram ta ce ita ke da alhakin kai hare- haren.

Tuni dai kungiyoyin da suka shirya gudanar da zanga- zangar kin jinin gwamnati a ranar Asabar a Legas suka soke gudanar da ita saboda tsoron yiwuwar barkewar wani tashin hankalin.

Karin bayani