'Ayyukan agaji na fuskantar barazana a Sudan ta Kudu'

Hakkin mallakar hoto spl arrangement
Image caption Mayakan kabilu a Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa ayyukan agajin gaggawa za su kara yin muni a Sudan ta Kudu sakamakon fadace-fadacen kabilanci da aka shafe mako da makonni ana gwabzawa.

An kiyasta cewa sama da mutane dubu dari da ashirin ne ke bukatar taimako a kasar.

Wani fada ya barke tsakanin kabilun Lu Nur da Murle a watan da ya gabata a jahar Jonglei, sakamakon harin da kabilun biyu suka rika kaiwa shanun junansu.

An hallaka mutane da dama a rikicin kuma wasu dubun- dubatar mutanen sun tsere

Jami'an majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu sun musanta zargin da ake yi cewa aikin da suke yi ba ya sauri, kuma ma bai wadata ba.