Newt Gingrich ya doke Romney a Carolina

Hakkin mallakar hoto cnn
Image caption Newt Gingrich

Newt Gingrich ya doke Mit Romney a zaben baya bayannan na fitar da mutumin da zai yi takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican.

A baya dai Mr Gingrich bai taka rawar a-zo-a-gani ba.

Kafin wannan lokaci dai Mr Mit Romney ne ke kan- gaba wajen yin takara a karkashin jam'iyar, sai dai wakilin BBC a jihar South Carolina ya ce abubuwa sun sauya yanzu.

Mr Mit Romney bai taya abokin hamayyarsa murna ba, sannan bai ambaci sunansa a cikin jawabinsa ba.

Dukkanin 'yan takarar hudu da suka hada da dan majalisa Ron Paul sun yi hasashen cewa za a dade ana fafatawa wajen neman wanda zai yiwa jam'iyar takara.