Shugaba Jonathan ya sha alwashin murkushe 'yan Boko Haram

Shugaba Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Jonathan

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi alkawarin murkushe wadanda suka kai hare-haren bama-bamai a birnin Kano, wadanda suka yi sanadiyyar hallaka akalla mutane dari da hamsin.

Yayinda yake magana a lokacin wata takaitacciyar ziyarar da ya kai birnin, Mr Jonathan ya ce hare-haren da aka kai ranar Juma'ar da ta gabata, tamkar an kai su ne a kan dukkan 'yan Najeriya.

Kungiyar nan ta Jama'atu Ahli sunna Lid Da'awati wal Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram, ta ce ita ce ta kai hare haren na Kano.

Ziyarar ta shugaba Jonathan dai ta zo ne a daidai lokacin da akalla mutane 11 suka rasa rayikansu yayinda wasu 'yan bindiga suka kai hari a kan wani ofishin 'yan sanda a garin Tafawa Balewa na jihar Bauchi.

Bayan Sakataren harkokin wajen Burtaniya, William Hague, shi ma Babban Sakataren majalisar dinkin duniya, Ban ki moon ya yi Allah wadai da hare- haren na ranar juma'a.

Karin bayani