Ana yamutsi a Libya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan tawaye a Libya

Masu zanga- zanga cikin fushi a garin Bengazi na Libya sun kutsa kai cikin hedikwatar gwamnatin rikon kwaryar kasar, bayan sun shafe sa'oi da dama suna yiwa ginin kawanya

Ganau sun ce daruruwan matasa, wadanda suka hada da tsofaffin mayakan da suka samu raunuka a lokacin yakin basasar kasar, sun yi amfani da duwatsu da karafa wajen karya kofar shiga hedikwatar.

Masu zanga- zangar na korafin cewa sabuwar gwamnatin Libyan na nuna musu wariya, sannan sun zargi shugabannin kasar da rashin gudanar da mulki na gaskiya.

Gwamnatin rikon-kwaryar ce dai ta kifar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi bayan da suka zarge shi da gudanar da mulkin kama-karya.