'Yan tawaye na samun nasara a Syria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu 'yan tawayen Syria

'Yan tawayen Syria sun ce sojojin kasar da ke sauya sheka zuwa bangarensu sun karbe iko da garin Douma a ranar Asabar da daddare bayan sun gwabza fada da dakarun gwamnati.

Daya daga cikin masu fafutukar ya ce wannan shi ne karo na farko da 'yan tawayen suka yi yunkurin gwabzawa da sojojin kasar kai tsaye ba kamar yadda aka saba gani a baya ba.

Amma wata kungiya da ke kare hakkin dan adam a Syria ta ce bayan karbe iko da garin, sai kuma 'yan tawayen suka yanke shawarar su janye, saboda fargabar kada sojojin gwamnatin Syria su far masu.

Tunda farko dai, kungiyar ta ce mutane hudu ne suka mutu a garin na Douma, a lokacin da dakarun Syria suka bude wuta akan wasu masu jana'iza.